Isa ga babban shafi
Thailand

Kungiyar yankin Asiya ta nemi sulhu a Thailand

Kungiyar ci gaban kasashen yankin kudancin Asiya ta bukaci bangarorin da ke da hannu a rikicin kasar Thailand da su bi hanyoyin sulhu domin warware sabanin da ke tsakaninsu.

Magoya mayan Hambararriyar Firaministan Thailand
Magoya mayan Hambararriyar Firaministan Thailand REUTERS/Chaiwat Subprasom
Talla

Sanarwar da ministocin harkokin wajen kasashen yankin suka fitar a a jiya lahadi bayan kammala wani taro a kasar Myanmar, kungiyar ta bukaci magoya baya da masu hamayya da tubabbiyar Firaminista Yingluck Shinwatra da su rungumi zaman lafiya a tsakaninsu.

Mambobin kungiyar sun jaddada bayar da goyon bayansu domin samar da zaman lafiya a wannan kasa da ke matsayin mamba a wannan kungiya.

Rikici ya sake kunno kai ne sakamakon zargin da magoya bayan tubabbiyar Firaministar suka yi zargin cewa ana shirin nada wani da zai fito daga bangaren adawa akan mukaminta.

Sai dai yan adawa sun bukaci a bai wa sabon Firaministan da ake shirin nadawa karfin ikon da zai tafiyar da kasar kafin shirya sabbin zabubbuka a cikin watanni 18 masu zuwa.

Magoya Shinawatra kuwa a taron gangamin da suka gudanar a karshen mako sun ce dole ne jagoran kasar ya kasance wanda al’umma suka zaba domin raba kasar daga fadawa cikin rikicin yaki.

Rikicin siyasa a Thailand ya raba kasar gida biyu bayan zaben Yingluck Shinawatra da ya biyo bayan hanbarar da dan uwanta Thaksin shinawatra a shekara ta 2006.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.