Kotun Thailand ta kori Shinawatra daga mukaminta
Kotun kundin tsarin mulkin kasar Thailand ta kori Firaministan kasar Yingluck Shinawatra daga Ofishinta, saboda ta yi amfani da karfi wajen sauya wajen aikin babbar Jami’ar tsaro Thawil Piliensri da ‘Yan adawa suka nada a 2011. Wannan hukuncin na kotun na zuwa ne a yayin da kasar ke cikin rikicin Siyasa.
Wallafawa ranar:
‘Yan adawa a kasar sun kwashe watanni suna gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnarin Yingluck tun a watan Nuwamban bara.
Kodayake, wannan hukuncin na kotun na iya haifar da rikici a kasar tsakanin magoya bayan Shinawatra da kuma ‘Yan adawa.
Akwai alamun Ministocin da suka amince da matakin sauya wajen aikin babbar Jami’ar tsaron zasu rasa mukaminsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu