Thailand
Kotu ta haramta zaben Thailand
Kotun duba tsarin mulki a kasar Thailand ta haramta zaben kasar da aka gudanar watan jiya, bayan an kwashe makwanni ‘yan adawa na zanga-zanga a fadin kasar. Kotun tace zaben ya sabawa kundin tsarin mulki saboda akwai yankunan da ba a gudanar da zaben ba.
Wallafawa ranar:
Talla
‘Yan adawa dai sun kauracewa zaben sannan masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin Yingluck Shinawatra suka hana a gudanar da zaben a wasu runfunan zabe.
Zuwa yanzu babu wata rana da aka kebe domin gudanar da sabon zabe a kasar Thailand da ke fama da rikicin siyasa tun a watan Nuwamban bara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu