Isa ga babban shafi
Thailand

An samu asarar rayukan jama'a a zanga-zangar Thailand

An kashe dan sanda daya da kuma wani farar hula a birnin Bangkok na kasar Thailand a wata arangamar da aka yi tsakanin masu zanga-zangar kin jinin gwamnati da kuma jami’an tsaro a wannan talata.

Manona na zanga-zanga a Bangkok na kasar Thailand
Manona na zanga-zanga a Bangkok na kasar Thailand REUTERS/Chaiwat Subprasom
Talla

Magoya bayan ‘yan adawa sun mamaye da dama daga cikin ma’aikatun gwamnati, yayin da daruruwan ‘yan sanda suka yi yunkurin tarwatsa su, to amma duk da haka sai da aka shiga tattauna kafin ‘yan adawar su janye daga harabar gine-ginen.

Firaminista Yingluck Shiniwatra, ta gabatar da jawabi ta talabijin ga manoman shinkafa na kasar wadanda su ma ke zanga-zanga domin neman gwamnatin ta biya su kudaden tallafi da ya kamata a biya su, wata alama ta neman kara kwantar da hankulan jama’a.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.