Isa ga babban shafi
Thailand

'Yan adawan kasar Thailand sun ci gaba da boren neman kifar da gwamnati

A yau Litinin masu zanga zanga a kasar Thailand, sun mamayen manyan titunan birnin Bangkok, a yunkurin sun a hana ruwa gudu a lamuran kasar. Wannan matakin ya kara zafafa yunkurin ‘yan adawa ma kifar da gwamantin Friminista Yingluck Shinawatra.Dubun dubatar mutane, dauke da tuta sun ja daga a mahadar hanyoyin birnin, inda wasu ke karkafa wuraren gangami da na kwana tare da wuraren cin abinci na kyauta.Masu zanga zangar na kokarin ganin Priminista Yingluck Shinawatra ta yi murabus, don majalisar rikon kwarya, da ba zabar ta aka yi ba, ta sami damar yin gyare gyare a tsarin mulkin kasar.‘Yan adawan suna ganin wannan matakin zai kawo karshen kakagidan da dangin Shinawatra, masu dukiya ke yi a fagen siyasar kasar, tare da yin waje rod da siyasar amfani da kudi.Waji jagoran masu zanga zangar Suthep Thaugsuban, yace yau rana ce mai cike da tarihi a kasar ta Thailand, inda ya lashi takobin ci gaba da bore har sai gwamnatin Yingluck ta fadi.‘Yan adwan sun kuma yi barazanar yin kafar ungulu a zaben da ake shirin yi a watan Fabrairu mai zuwa. 

Masu zanga zangar kasar Thailand sun rufe hanyoyi
Masu zanga zangar kasar Thailand sun rufe hanyoyi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.