Isa ga babban shafi
Thailand

‘Yan adawa sun kaddamar da gagarumar zanga-zanga a Thailand

‘Yan adawa a kasar Thailand, sun kaddamar da wata gagarumar zanga-zanga da nufin kawo karshen mulkin Firaminista Yingluck Shinawatra kafin a gudanar da sabbin zabuka a kasar. Daruruwan masu zanga-zangar ne suka mamaye birnin Bangkok inda komi ya tsaya cak a babban birnin kasar.

Daruruwan masu zanga zanga da suka mamaye Birnin Bangkok domin adawa da gwamnatin Firaminista Yingluck Shinawatra
Daruruwan masu zanga zanga da suka mamaye Birnin Bangkok domin adawa da gwamnatin Firaminista Yingluck Shinawatra REUTERS/Athit Perawongmetha
Talla

Masu zanga-zangar suna neman Firaminista Yingluck Shinawatra ta yi murabus domin kafa gwamnatin rikon kwarya da zata kula da sabbin sauye sauyen dokokin zabe da Firaministar ke shirin gudanarwa a ranar 2 ga watan Fabrairu.

Tun a daren Lahadi masu adawa da gwamnatin suka soma kange manyan titunan birnin na Bangkok, a wani mataki da suka bayyana shi da cewa shi ne yunkurin karshe domin kawo karshen mulkin Shinawatra.

Tun Kafin wannan lokaci, abokannin hamayya na siyasa sun share tsawon makwanni suna shirya tarzoma musamman a birnin na Bangkok, lamarin da ya tlisata wa Firaministar rusa majalisar dokoki da kuma kiran zaben gaggawa.

Jagoran ‘yan adawar Suthep Thaugsuban, ya ce ba su da niyyar shiga tattauwa da gwamnati a game da wannan manufa ta su, yana mai cewa barin Firaminista akan mukaminta tamkar dawowa ne Dan uwanta tsohon Firaminsta Taksin Shinawatra.

Thailand kasa ce da ta fuskanci juye-juyen mulki ko dai na soja ko kuma bisa umurnin kotu har sau 18 daga lokacin samun ‘yanci daga shekarar 1938 zuwa yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.