Isa ga babban shafi
Thailand

‘Yan bindiga sun bude wuta a sansanin 'Yan adawa a Thailand

A kasar Thailand, wasu mutane dauke da makamai sun kai hari akan wani sansani da ‘yan adawa suka kafa a birnin Bangkok inda suka buda wuta tare da raunata mutane da dama a cikin daren Juma’a.

Daruruwan masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Thailand a Bangkok
Daruruwan masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Thailand a Bangkok REUTERS/Athit Perawongmetha
Talla

Hukumomin tsaro a birnin sun tabbatar da faruwar wannan lamari, da ke zuwa a daidai lokacin da masu adawa da Firaminista Yingluck Shiniwatra suka kuduri aniyyar kaddamar da wani gagarumin bore domin kawo karshen gwamnatinta a ranar litinin mai zuwa.

Yanzu haka dai an sanya jami’an tsaro da suka hada har da sojoji da yawansu ya kai dubu 20 a cikin shirin ko ta-kwana a birnin na Bangkok.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.