‘Yan bindiga sun budewa gangamin ‘Yan adawa wuta a Thailand
Wasu ‘Yan bindiga sun bude wa gangamin ‘Yan adawa wuta a kasar Thailand wanda ya kara hura wutar rikicin kasar inda ake zanga-zangar kin jinin gwamnatin Firaminista Yingluck Shinawatra. Rahotanni sun ce mutum guda ya mutu wasu da dama kuma sun samu rauni.
Wallafawa ranar:
Masu zanga zangar da suka yi sansani a kusa da cibiyar gwamnati a birnin Bangkok na kasar Thailand a daren Juma’a zuwa safiyar Assabar sun fuskanci harbin bindiga da ya yi sanadiyar mutuwar mutum guda kamar yadda jami’an kai dauki suka tabbatar
Wadanda suka bayyana cewa, wasu mutanen 3 da suka jikkata a sakamakon harbin an kwantar da su a asibiti
Wannan hari ya zo ne kwanaki biyu da faruwar tashin hankalin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 2 da suka hada da Dan sanda guda da wani mai zanga zanga, a yayinda wasu 150 suka jikkata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu