Isa ga babban shafi
Thailand

Yingluck ta rusa majalisar Thailand don a gudanar da zabe

Firaministan kasar Thailand Yingluck Shinawatra ta rusa majalisar kasa tare da kiran a gudanar da zabe sakamakon jerin zanga-zangar kin jinin gwamnati da ake yi a kasar. Wannan matakin na zuwa bayan ‘Yan adawa a majalisar kasar sun yi murabus a ranar Lahadi.

Dubban Masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin Shinawatra a Bangkok
Dubban Masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin Shinawatra a Bangkok REUTERS/Damir Sagolj
Talla

Akalla mutane Dubu dari da arba’in ne  suke gudanar da zanga-zanga a Bangkok babban birnin Thailand don tursasawa Firaministan Yingluck Shinawatra ta sauka daga kan mulki.

A shekarar 2011 ne Shugaba Yingluck ta lashe zaben shugaban kasa, amma masu zanga-zangar sun ce yayanta ne Thaksin Shinawatra ke jan ragamar shugabancin kasar wanda aka hambarar da gwamnatinsa.

Majiyar 'yan sanda ta tabbatar da cewar an samu fitowar mutane daga karfe 10 na Safiyar Litinin a babban birnin kasar Bangkok .

Yingluck Shinawatra ta dauki matakin rusa Majalisar dokokin kasar ne  a yau Litinin, tare da kiran zaben gaggawa domin kawo karshen rikicin siyasar da ake fama da shi a kasar.

A jawabin da ta gabatar ta kafafen yada labaran kasar, Shinawatra ta ce ta dauki wannan mataki ne bayan da ta tattauna da mukarrabanta kan yadda za a warware wannan rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.