Isa ga babban shafi
Thailand

An bayar da sammacin kama shugaban 'yan adawar Thailand karo na biyu

Kotu a kasar Thailand ta bayar da sammaci kama shugaban masu zanga-zangar nuna kyamar gwamnati da ake gudanarwa a kasar, bisa zargin cewa yana neman tumbuke zababbiyar gwamnatin dimokuradiyyar ta Fira minista Yingluck Shinawatra ne.

Masu zanga-zanga a kasar Thailand
Masu zanga-zanga a kasar Thailand
Talla

An dai bayyana cewa tasirin iyalan Gidan Shinawatra a fagen siyasar kasar ta Thailand ne ya haifar da tarzomar da ake fama da ita a kasar a wannan lokaci.

Yanzu haka dai masu zanga-zangar dai na ci gaba da kone-kone a kan titunan birnin Bangkok, yayin da jami'an tsaro ke kokarin tarwatsa su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.