Isa ga babban shafi
Thailand

Zanga zanga ta yadu a kasar Thailand

Zanga Zangar da ake yi a kasar Thailand tare da mamaye ofisoshin gwamnati ta yadu zuwa wasu garuruwan kasar, yayin da yau aka shiga rana ta uku. 

Masu zanga-zanga a Thailand
Masu zanga-zanga a Thailand REUTERS
Talla

Masu zanga zangar na adawa ne da matakan da gwamnatin Fira Minista, Yingluck Shinawatra ke dauka, da kuma shirin yiwa Dan uwan ta kuma tsohon Fira Minista, Thaksin Shinawatra ahuwa.

Wannan zanga na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin kasar ke fuskantar rashin amincewa da rikon ludayinta a majalisar kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.