Isa ga babban shafi
Thailand

Ana zanga-zangar kin jinin gwamnati a Thailand

Dubun dubatar ‘Yan kasar Thailand ne suka ci gaba da zanga zanga a birnin Bangkok, a wani gangamin siyasar da aka ce ya fi kowanne tasiri a kasar, tun bayan wanda aka yi a shekarar 2010, da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Dubban Masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Bangkok
Dubban Masu zanga-zangar kin jinin gwamnati a Bangkok REUTERS/Damir Sagolj
Talla

‘Yan sanda sun kiyasta kusan mutane dubu 90, ne masu adawa da gwamnatin Firaminista Yingluck Shinawatra, ke dandazo a wurare daban daban har guda uku.

Masu zanga zangar na neman a kifar da gwamnatinta, yayin da a wani bangaren kuma ‘yan kungiyar nan ta masu jar Hula su kusan dubu 50, ke nuna goyon bayansu ga gwamnatin.

Dukkan bangarorin sun lashi takobin ci gaba da kasancewa a kan titunan birnin Bangkok, da a baya aka yi ta samun tashe tashen hankula, tun bayan kifar da gwamnatin tsohon Fimiya Thaksin Shinawatra, da soja suka hambarar shekaru bakwai da suka gabata.

Lokacin da ya ke jawabi ga magoya bayan su da suka raba dare a kan titunan kasar, tsohon mataimakin Friminista Suthep Thaugsuban, ya nemi su ci gaba da jajircewa.

A halin da ake ciki yau litinin masu zanga zangar sun afka ma’aikatar kudin kasar, tare da barazanar sake kame wasu karin gine ginen gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.