Isa ga babban shafi
Thailand

An Tuhumi tsohon Firaministan Thailand da kashe masu zanga-zanga

Hukumomin Kasar Thailand, sun tuhumi tsohon Firaministan kasar, Abhisit Vejjajiva, da laifin kashe mutane kusan 90, wadanda suka mutu sakamakon kazamar zanga zangar da magoya bayan Thaksin Sinawatra suka yi a shekarar 2010.

Tsohon Firaministan kasar Thailand Abhisit Vejjajiva
Tsohon Firaministan kasar Thailand Abhisit Vejjajiva Reuters/Sukree Sukplang
Talla

Ana zargin tsohon Firaministan ne da bai wa sojoji umurnin amfani da karfin da ya wuce kima, wajen kashe masu zanga zangar, da kuma raunana wasu 1,900.

A bangare daya kuma, ana tuhumar shugabanin magoya bayan Thaksin Sinawatra 24 da aikata ta’addanci, cikinsu har da ‘Yan Majalisu guda biyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.