Isa ga babban shafi
Thailand

Wasu ‘yan Jarida na daga cikin mutane 10 da suka jikkata a tashin Bomb na kasar Thailand.

Wasu Tagwayen Boma-Bomai 2 ne suka tashi a yankin Kudancin kasra Tahiland ya kuma jikkata mutane 10 kusan rabin su ‘yan Jarida ne ciki kuwa hada mai daukat Hoto na Kamfanin dillancin labarai na AFP.

Kasar Thailand
Kasar Thailand
Talla

Jami’an ‘yan sanda dai sun tabbatar da wannan labarin kuma tashin Bomb na farko ya faru ne a Narathiwat da sanyin safiyar Assabar.

Jami’an ‘yan sandan haka ma sun bayyana cewar a karon far akwai wasu ‘yan tsagera da suka kai hari wa Jami’an Soji tare da jikkata akalla Soji Shida.

‘Yan Jaridra da suka tasarwa wurin da Bomb din farko ya tashi sun tsaya ne nesa da inda abin ya faru, amma kuma sai ga wani Bomb din ya tashi a kusa da su.

Madaree Tohala mai daukar Hoto na AFP y ace ba ai iya tuna yanda abin ya faru ba, saboda suna zantawa ne kawai a gefen Titi, suna jiran hukumomio su yi masu bayanin yanda al’amarin yake, lokacin da Bomb din ya tashi ya kuma jikkata da dama daga cikin su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.