Isa ga babban shafi
Thailand

Ƴan Sanda sun yi arangama da masu zanga-zanga a Thailand

Aƙalla mutane uku suka mutu, wasu da dama ne kuma suka jikkata sakamakon arangama da aka yi tsakanin Ƴan sanda da masu zanga-zanga a birnin Bangkok na ƙasar Thailand. Sabon rikicin ya ɓarke ne a lokacin da Ƴan sanda suke ƙoƙarin tarwatsa sansanin masu zanga-zanga.

Masu zanga-zanga a Thailand
Masu zanga-zanga a Thailand REUTERS/Athit Perawongmetha
Talla

Yanzu haka kuma hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar Thailand tace zata caji Firaministan kasar Yingluck Shinawatra da ke fuskantar bore akan badakalar kuɗaɗen tallafin Shinkafa.

Wannan kuma na zuwa ne sa’o’I ƙalilan da ɓarkewar rikici tsakanin Ƴan sanda da masu zanga-zanga wadanda suka kwashe watanni suna adawa da gwamnati.

Masu zanga-zangar sun mamaye gine ginen gwamnati ne tun a watan Nuwamba suna masu neman lalle sai an samu sauyin gwamnatin. Tuni kuma gwamnatin ta bayar da sanarwar tarwatsa masu zanga-zangar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.