Kwamandan Soja ya gana da ‘Yan siyasa a Thailand
Shugaban rundunar sojan kasar Thailand ya jagoranci wani taro, da shugabannin ‘yan siyasar kasar da basa ga maciji da juna. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara afni da wata dokar soja, da nufin hana barkewar tashe tashen hankula a kasar.
Wallafawa ranar:
An shafe fiye da sa’oi biyu ana gudanar da taron, kuma ya sami halartar bangarorin da ke hamayya da juna, tare da manyan jami’an gwamnatin kasar.
Taron da aka yi a birnin Bangkok, karkashin jagorancin kwamandan sojan kasar, Prayut ya gudana ne cikin tsauraran matakan tsaro, da wani mai goyon bayan zababbiyar gwamnatin kasar ya bayyana da yanayi mai inganci.
Rashin cimma matsaya a taron na jiya Laraba, yasa aka yanke shawarar ci gaba da zaman a yau Alhamis.
Rikicin siyasan kasar ta Thailand na afkuwa ne tsakanin gidan sarautar Bangkok da masu goya musu baya a bangare daya, da iyalan tsohon Firaminista Thaksin Shinawatra, attajirai da ke matukan samun goyon bayan al’ummar arewacin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu