Isa ga babban shafi
Thailand

Sojoji sun yi wa 'yan siyasa kashedi a Thailand

Babban kwamandan askawaran kasar Thailand ya yi barazanar cewa sojoji za su yi amfani da karfi domin kawo karshen rikicin siyasar da kasar ke fama da shi yau kusan watanni hudu kenan.

Kwamandan sojan Thailand, Janar Prayuth Chan-ocha
Kwamandan sojan Thailand, Janar Prayuth Chan-ocha (Reuters)
Talla

Babban kwamandan askarawan kasar Janar Prayut Chan-O-Cha, ya ce ba za su zura ido ‘yan siyasa na ci gaba da yin garkuwa da kasar ba, inda ya ce ‘’ ina mai gargadin dukkanin bangarorin da ke da hannu a wannan rikici musamman wadanda ke amfani da makamai a kan fararen hula, da su kawo karshen hakan ko kuma sojojin su fito don wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.’’

Janar Chan-0-Cha, wanda ke gargadi jim kadan bayan da hukumar zaben kasar ta bukaci a dage gudanar da zabubuka a cikin watan yuli mai zuwa saboda tashe-tashen hankula, ya ce dole ne sojoji sun yi amfani da matsayinsu wajen tabbatar da doka da odo a fadin kasar ta Thailand.

A ciki da wajen kasar dai ana kallon janar Chan-O-Cha a matsayin wanda ya taka rawa gagarumar wajen kawo karshen mulkin tsohon firaministan Taksin Shinawatra a shekara ta 2009, inda sojoji suka yi amfani da karfi domin murkushe masu tarzoma har ma aka sami asarar rayukan mutane 91 da kuma raunata wasu akalla 1.800.

Duk da cewa kotun tsarin mulkin kasar ta tube firaminista Yingluck Shinawatra daga mumakinta, to amma har yanzu ana ci gaba da takaddama tsakanin magoya bayanta da kuma ‘yan adawa kan yadda za a zabo wanda zai maye gurbinta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.