Isa ga babban shafi
Thailand

Kalubalen da ke gaban sabon Firimiyan Thailand

Bayan da babbar kotun shari’ar kasar Thailand ta tsige Firaministar Kasar Yingluck Shinwatra a makon da ya gabata, hukumomin kasar sun nada Niwattumrong Boosongpaisan a matsayin sabon Firaminista.

Masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin Thailand
Masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin Thailand EUTERS/Athit Perawongmetha
Talla

Sabon Firaministan wanda ake kira Niwattumrong Boosongpaisan, ya kasance yana rike da mukaman Minista ne a ma’aikatar kasuwancin kasar da kuma mataimakin Firaminista, an kuma yi maza maza ne aka mai karin girma bayan da aka tsige Yingluck Shinwatra daga mukaminta.

An haifi Boosongpaisan ne a ranar 25 ga watan Janairun shekarar 1948 ya kuma yi karantunsa ne a fannin ilmantarwa. Ya kuma rike ma’aikatu da dama tsakanin 1993 zuwa 2003.

A watan Yunin shekarar 2013, Shinwatra ta ba shi mukamin mataimakin Firaminista da kuma ministan ma’aikatar kasuwanci.

Sai dai a yanzu haka, duk da cewa an hambarar da Shinwatra, hakan bai hana mutanen kasar ci gaba da yin bore ba, wanda haka wasu ke kallo a matsayin babban kalubale ga sabon Firaministan, yayin da ya mika goron gayyata ga ‘yan adawa tare da yunkurin ganin an gudanar da zaben da za a yi a ranar 20 ga watan Yuli mai zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.