Isa ga babban shafi
Thailand

An daure wani shekaru 30 saboda ya zagi Sarkin Thailand a Facebook

Kotun Soji a kasar Thailand ta yanke wa wani mutum hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari saboda ya wallafa hoto da wasu kalaman batanci ga Sarkin Bhumibol Abulyadej.

Sarkin Thailand Bhumibol Abulyadej.
Sarkin Thailand Bhumibol Abulyadej. Reuters
Talla

Sarkin mai shekaru 87 na da cikakkar kariya daga batanci karkashin dokar Thailand, kuma duk wani da aka kama ya zagi Sarki ko Sarauniya ko ‘yan gidan sarautar kasar zai fuskanci hukuncin daurin shekaru 15 ga duk batanci da ya aikata ga daya daga cikinsu.

Kotun ta ce ta kama mutumin mai suna Pongsak Sriboonpeng, dan shekaru 48 da laifin wallafa hotuna da sako sau shida a Intanet. Akan haka aka yanke masa hukunci ga duk sakon da ya wallafa.

Kuma a tsarin Dokar Thailand mutum bai iya daukaka kara idan Kotun Soji ta yanke hukunci, a cewar lauyan da ke kare Sriboonpeng.

A ranar alhamis ma kotun ta kama wani da laifin lalata hoton Sarki da Sarauniyarsa.

Wannan hukuncin dai na daga cikin mafi tsauri da mahukuntan Sojin Thailand suka zartar tun kwace mulki a 2014.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.