Isa ga babban shafi
Thailand

Sojojin Thailand sun haramtawa ‘Yan siyasa ficewa kasar

Gwamnatin mulkin sojan kasar Thailand ta haramta wa ‘Yan siyasa 155 ficewa kasar, da suka hada da shugaban kasa da manyan tsofaffin jami’an gwamnati. Rahotanni kuma sun ce a Yau Juma’a tsohuwar Firaministar Kasar, Yingluck Shinawatra ta gurfana a gaban jami’an sojan da suka karbe gwamnatin kasar.

Babban kwamandan Sojan Thailand Prayuth Chan-ocha.
Babban kwamandan Sojan Thailand Prayuth Chan-ocha. AFP PHOTO / PORNCHAI KITTIWONGSAKUL
Talla

Akwai kuma karin wasu ‘Yan siyasar da jami’an na Sojan kasar suka umarci su gurfana.

A ranar Alhamis ne Sojoji suka kwace mulki saboda rudanin siyasa da kasar ta shiga.

Kasashen duniya da dama ne suka yi Allah wadai da juyin mulkin da Sojoji suka yi a aka Thailand.

Wata ‘Yar kasar Thailand mai suna Fey Subathana ta shaidawa gidan Rediyo Faransa cewa suna bukatar neman sojoji su janye daga fagen siyasar kasar, domin abin da suke bukata shi ne a gudanar da zabe, wanda ta hakan ne kasar za ta koma kan turbar dimokuradiyya kamar yadda kundin tsarin mulkinta ya tanada.

Amurka tace tana nazarin diba dangantakarta da Thailand sakamakon juyin mulkin.

Kasar Faransa da Birtaniya da kungiyar Tarrayar Turai sun yi tir da wannan mataki na soji a Thailand tare da yin kira ga kasar ta koma kan turbara demokuradiya.

An dai share tsawon watanni kasar na fama da rikicin siyasa, lamarin da ya sa kotun kolin kasar ta tube Firaminista Yingluck Shinawatra daga karagar mulki, amma duk da haka an ci gaba da samun rikici tsakanin magoya bayanta da kuma ‘yan hamayya, inda daga karshe sojoji suka sanar da kwace mulkin kasar a ranar Alhamis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.