Isa ga babban shafi
Thailand

Kasashen duniya sun bukaci Thailand ta dawo kan turbar dimokuradiyya

Kungiyar Tarayyar Turai ta yi tir da kuma Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Thailand, inda kungiyar ta bukaci a gaggauta dawo da kasar kan turbar dimokuradiyya. 

Sojoji kan titunan birnin Bangkok na Thailand
Sojoji kan titunan birnin Bangkok na Thailand
Talla

Shugabar ofishin kare manufofin ketare a Kungiyar Cathrine Ashton, ta bakin wani mai magana da yawunta, ta bayyana cewa dole ne sojoji su gaggauta dawo da kasar akan mulki na dimokuradiyya.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya soki wannan juyin mulkin da aka yi a Thailand tare da yin kira da a mayar da kasar kan turbar dimokuradiyya kamar yadda kundin tsari mulki ya tanada.

An dai share tsawon watanni kasar na fama da rikicin siyasa, lamarin da ya sa kotun kolin kasar tube firaminista Yingluck Shinawatra daga karagar mulki, to amma duk da haka an ci gaba da samun rikici tsakanin magoya bayanta da kuma ‘yan hamayya, inda daga karshe sojoji suka sanar da kwace mulkin kasar a wannan alhamis.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.