Isa ga babban shafi

Indonesia ta dakatar da fitar da manja zuwa kasuwannin duniya

Gwamnatin Indonesia ta yanke shawarar hana fitar da manja daga ranar alhamis, saboda wahalar da 'yan kasar ke fuskanta wajen samunsa.

Wasu 'yan kasar Indonesia yayin da suka yi layin sayen manja saboda matsalar karancinsa da suke fuskanta.
Wasu 'yan kasar Indonesia yayin da suka yi layin sayen manja saboda matsalar karancinsa da suke fuskanta. AFP - ABDUL QODIR
Talla

Matakin na Indonesia kasar da ta fi kowacce kasa samar da albarkar manjan a duniya ya bijiro ne sakamakon fuskantar matsalar karancin man girkin a cikin gida da take yi da kuma hauhawar farashinsa, inda masu amfani manjan a garuruwa da dama sai sun yi jerin gwano na tsawon sa’o’i a gaban manyan rumbuna ko cibiyoyin adana kayayyakin bukata kafin su sayi manjan kan farashi mai rahusa.

Mahukunta a kasar ta Indonesia da ke kudu maso gabashin Asiya na fargabar cewa karanci da hauhawar farashin manjan na iya haifar da tarzoma a tsakanin jama'a.

Shugaban Indonesia Joko Widodo ya ce wadata ‘yan kasarsa akalla miliyan 270 shi ne babban burin gwamnatinsa, domin abin mamaki ne a ce, kasar ke kan gaba wajen samar da manjan a duniya amma kuma suna fama da karancinsa.

Indonesia na samar da kusan kashi 60 cikin 100 na manjan da ake samarwa a duniya, yayin da al’ummar kasar ke amfani da kashi 1 bisa uku na jumillar adadin manjan da ta samar.

Kasashen India, Pakistan, China, da kuma Tarayyar Turai na cikin manyan abokan cinikin da ke kan gaba wajen sayen manjan kasar Indonesia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.