Isa ga babban shafi
Indonesia

Masu linkaya sun soma ciro sassan jikin fasinjojin jirgin da ya fada teku

Rahotanni daga Indonesia sun ce masu linkaya sun samu nasarar ciro wasu gawarwaki da kuma karin baraguzan jirgin saman fasinja kirar Boeing 737 da yayi fada cikin teku a jiya asabar, jim kadan bayan tashinsa daga birnin Jakarta.

Wasu daga cikin jami'an ceto masu a Indonesia yayin laluben baraguzan jirgin da ya fada teku a gaf da tsibirin Lancang
Wasu daga cikin jami'an ceto masu a Indonesia yayin laluben baraguzan jirgin da ya fada teku a gaf da tsibirin Lancang © Adek Berry / AFP
Talla

Masu bibiyar hadarin, sun ce jirgin mai dauke da fasinjoji 62 ya rikito ne mituna 4 bayan tashinsa, kuma an gano wasu sassan gawarwakin mutanen da ke cikinsa ne da kuma baraguzan jirgin daga zurfin mita 23 cikin tekun Java a gaf da tsibirin Lancang da ake yawon bude idanu.

Baki dayan fasinjojin da hadarin ya rutsa da su ‘yan kasar Indonesia ne, ciki har da kananan yara 10.

Sama da jami’an agaji 300 ne ke cigaba da laluben sauran gawarwakin fasinjoji da kuma sassan jirgin saman da ya rikito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.