Isa ga babban shafi
Faransa-Indonesia

Indonesia ta kulla yarjejeniyar sayen jiragen yaki 42 kirar Rafale daga Faransa

Indonesia ta kulla yarjejeniyar sayen jiragen yaki 6 kirar Rafale daga Faransa wanda ke matsayin wani bangare na jirage 42 da kasar ke shirin saye dai dai lokacin da Paris ke karfafa alakarta da kasashen Asiya.

Jiragen yakin Rafale kirar Faransa.
Jiragen yakin Rafale kirar Faransa. CHAIDEER MAHYUDDIN AFP/File
Talla

Bangarorin biyu sun sanar da yarjejeniyar ne yayin ganawar ministar tsaron Faransar Florence Parly da na Indonesia Prabowo Subianto a birnin Jakarta yayin ziyarar da babbar jami’ar ta Paris ke kaiwa kasar ta Asiya.

Acewar ministan tsaron na Indonesia, Jakarta ta aminta da sayen jiragen yaki 42 daga Faransa, amma karon farko za ta fara da guda 4 gabanin 36 wani lokaci a nan gaba.

Yarjejeniyar sayen jiragen da ke nuna kulluwar sabuwar alaka tsakanin Faransar da Indonesia na zuwa bayan rugujewar yarjejeniyar biliyoyin daloli ta sayen jiragen yakin karkashin teku tsakaninta da Australia.

Rushewar yarjejeniyar dai ta matukar fusata Faransa wanda ya sanya ta karkatar alakarta zuwa wasu yankuna don kange kasuwar makaman Amurka da Birtaniya a kasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.