Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta karbi rukunin karshe na jiragen yakin zamani kirar Super Tucano

Gwamnatin Najeriya ta sanar da karbar rukunin karshe na jiragen yakin zamani guda goma sha biyu kirar Super Tucano da ta saya daga kasar Amurka.

Jirgin yaki na zamani kirar Super Tucano A-29.
Jirgin yaki na zamani kirar Super Tucano A-29. DefenceTalk
Talla

Ministan watsa Labaran Najeriyar Lai Mohammed ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, lokacin wata zantawa da manema labarai.

A ranar 22 ga watan Yuli, rundunar sojin saman Najeriya ta karbi rukunin farko na jiragen yakin Super Tucano guda 6 daga cikin 12 da ta saya daga Amurka.

Yayin sanar da ci gaban da aka samu a jiya ne kuma Ministan yada labarai Lai Mohammed ya ce tuni aka tura dukkan jiragen zuwa yankin Arewa maso Gabashin Najeriya mai fama da rikicin Boko Haram.

Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed, yayin wani taron manema labarai a birnin Abuja.
Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed, yayin wani taron manema labarai a birnin Abuja. © REUTERS/Afolabi Sotunde

Ministan ya kuma bayyana mamakin rahoton da hukumomin tsaron Najeriya suka musanta, da ya ce rundunar sojin sama ta baiwa ‘yan bindiga naira miliyan 20 a matsayin cin hanci don kada su harbo da jirgin shugaban kasar, duk da irin nasarorin da sojoji suka samu a kan ‘yan ta’adda.

A cewar Lai Mohammed, abin tambaya game da waccan rahoto shi ne waye aka mika wa cin hancin a  tsakanin sansanonin ‘yan bindiga kusan 150 da ke tsakanin Zamfara, Katsina, da sassan jihohin Kaduna da Neja.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.