Isa ga babban shafi

Adadin wadanda girgizar kasa ta kashe a Turkiya da Syria ya kai dubu biyu

Wata kakkarfar girgizar kasa da ta afkawa kasashen Syria da Turkiya ta kashe mutane fiye da dubu 1 da 200 baya ga rushe tarin gidaje da sanyin safiyar yau litinin dai dai lokacin da ake fargabar yiwuwar ibtila’in ya shafi wasu yankuna na tsibirin Cyprus da Masar da kuma Lebanon wadanda suka jiyo motsinta.

Yankunan da girgizar kasa ta yiwa barna a Syria da Turkiya.
Yankunan da girgizar kasa ta yiwa barna a Syria da Turkiya. AP - Elifaysenurbay
Talla

Sanarwar ma’aikatar lafiyar Syria ta bayyana cewa mutum 473 girgizar kasar ta kashe a iya yankunan da ke karkashin kulawar gwamnati, baya ga wasu dubunnai da suka jikkata yayinda bayanai ke cewa a yankunan ‘yan tawayen kurdawa ibtila’in ya kashe tarin mutanen da babu cikakken alkalumansu.

Girgizar kasar mai karfin maki 7.8 ta afkawa yankunan da ke iyakar kasashen biyu ne da kuma yankunan da ke karkashin ikon gwamnatin Syria da suka kunshi Aleppo da Alatakia da Hama da kuma Tartus lamarin da ya sanya fargabar yiwuwar ta tsallaka tsibirin Cyprus da kuma Masar.

Tun da misalin karfe 4 na asubahi girgizar kasar ta dirarwa yankunan Gazantep mai yawan jama’a miliyan 2 a Turkiya inda hukumar kula da bala’o’I ta kasar ke cewa yanzu haka aka zakulo gawarwakin mutane 912 baya ga jikkatar wasu dubu 3 da 323.

Tuni kasashen Duniya suka fara mikawa kasashen biyu tayin kai musu dauki ciki har da Amurka da ta ce a shirye take ta kawo dauki ga wadanda ibtila’in ya shafa yayinda shugaba Recep Tayyib Erdogan na Turkiya ya sanar da aike jami’ai na musamman don bayar da kulawa da kuma aikin ceto wadanda ibtila’in ya rutsa da su.

Yanzu haka dai jami'an agaji daga kasashen Faransa da Tarayyar Turai sun isa kasashen biyu don kai daukin gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.