Isa ga babban shafi

Shugaba Lula zai nada ministoci 37, a maimakon 23 na Bolsonaro

Gwamnatin zababben shugaban kasar Brazil Lula za ta fi samun yawan kujeru na ministoci fiye da na Jair Bolsonaro mai barin gado, tare da ma'aikatu 37, a kan 23 kacal a halin yanzu.

Sabon Shugaban Brazil Luis Inacio Lula da Silva .
Sabon Shugaban Brazil Luis Inacio Lula da Silva . Reuters
Talla

Kujerun Ministocin zai karu da kashi 60% a wa'adi na uku na Luiz Inacio Lula da Silva, wanda zai fara aiki a ranar 1 ga watan Janairu, tawagarsa ta ba da tabbacin cewa yawan ma'aikatan da ke aiki a ma'aikatun ba za su canza ba.

Sabon shugaban kasa Luiz Inacio Lula da Silva ya bukaci a ruguza ma’aikatun, amma ba tare da samar da karin mukamai ba, adadin kudaden da za a kashe za su kasance iri daya, ba tare da la’akari da adadin ma’aikatun ba. Kuma Luiz Inacio Lula da Silva ya yanke shawarar samar da kujerun ministoci 37.

Rui Costa, wanda zai zama daya daga cikin ministan Luiz Inacio Lula da Silva ne ya shaida wa manema labarai tsarin da shugaban ke da shi.

A cewarsa, tsarin gwamnati zai kasance mai “canzawa” kuma ma’aikatan gwamnati da yawa za su yi aiki a ma’aikatu da dama, wanda hakan zai sa a iya ceton ma’aikata.

Lula, mai shekaru 77, zai koma ofishin koli bayan shekaru ashirin da barinsa, bayan wa'adi biyu na farko 2003 da 2010.

A karo na biyu, gwamnatinsa tana da ma'aikatu 37.

A lokacin, tattalin arzikin yana bunƙasa, godiya ga haɓakar kayayyaki wanda ya ba wa hagu damar aiwatar da shirye-shiryen zamantakewa.

Amma yanayin tattalin arziki ya sha bamban sosai a farkon wa'adinsa na uku kuma 'yan kasuwa na fargabar cewa sabuwar gwamnatin Lula za ta yi watsi da tabarbarewar kasafin kudi.

Rui Costa, tsohon gwamnan jihar Bahia da ke yankin arewa maso gabas, ya nuna cewa za a sake kirkiro ma'aikatun Kifi, Birni da Wasanni, wadanda suka bace a karkashin Bolsonaro.

Ma'aikatar Tattalin Arziki za ta wargaje, tsakanin Kudi, Tsare-tsare, Gudanarwa da Ci gaba, da kuma Kasuwanci da Masana'antu.

Haka za ta kasance ta bangaren ababen more rayuwa, ta rabu gida biyu, a daya bangaren kuma ma’aikatar sufuri, wadda za ta hada da tituna da layin dogo, sannan a daya bangaren ma’aikatar tashoshi da tashoshin jiragen sama.

Rui Costa ya kuma tabbatar da samar da ma'aikatar 'yan asalin kasar, wacce wani dan asalin kasar zai jagoranta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.