Isa ga babban shafi

Zababben shugaban Brazil Lula ya fashe da kuka

Zababben shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya fashe da kuka yau litinin, lokacin da kotun koli ta amince da zaben da aka masa a matsayin shugaban kasa sakamakon nasarar zaben da ya samu domin yin wa’adi na 3.

Lokacin da Lula ke karbar takardar shaidar nasarar zabensa
Lokacin da Lula ke karbar takardar shaidar nasarar zabensa REUTERS - UESLEI MARCELINO
Talla

Bayan karbar takardar shaidar nasarar zaben da aka gudanar a ranar 30 ga watan Oktoba, Lula mai shekaru 77 cikin hawaye ya jinjinawa mutanen Brazil akan yadda suka sake bashi jagorancin kasar duk da rashin samun ilimin da zai bashi damar samun shaidar difloma daga jami’a.

Ana saran rantsar da Lula a ranar 1 ga watan gobe domin maye gurbin shugaba Jair Bolsonaro da ya kayar a zagaye na biyu na zaben da suka fafata.

Wannan ba karamar nasara bace ga Lula wanda ya jagoranci Brazil har sau biyu, tsakanin shekarar 2003 zuwa 2010, ya kuma bar karagar mulki a matsayin shugaban kasa mafi farin jinni a tarihin kasar, kafin daga bisani a daure shi na watanni 18 saboda zargin cin hanci daga badakalar kamfanin man fetur din kasar.

Lula wanda yaki amincewa da zargin ya bar gidan yari ne a watan Nuwambar shekarar 2019 lokacin da kotun kolin Brazil ta wanke shi daga tuhumar da aka masa, abinda ya bashi damar sake tsaya takara.

Shugaban mai jiran gado ya bayyana hukuncin kotun zaben a matsayin babbar nasara ga dimokiradiya, bayan da Bolsonaro yayi watsi da sakamakon zaben, yayin da dubban magoya bayansa suka tare hanyoyin mota da kuma guda zanga zangar tare da kiran sojoji da su sanya baki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.