Isa ga babban shafi

EU za ta sake lafta takunkumai kan Iran saboda taimakawa Rasha da makamai

Kungiyar Tarayyar Turai ta sanar da shirin sake laftawa Iran sabbin takunkuman karya tattalin arziki sakamakon yadda kasar ke taimakawa Rasha da jirage marasa matuki da ake amfani da su wajen kai hare-hare sassan Ukraine.

Wasu nau'ikan jirage marasa matuka samfurin Iran.
Wasu nau'ikan jirage marasa matuka samfurin Iran. AP
Talla

Kungiyar ta EU na sanar da wannan mataki ne gabanin taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da zai tattauna kan sabbin hare-haren da Rasha ta zafafa kaiwa sassan Ukraine cikin kwanakin nan.

Mai magana da yawun hukumar ba da agajin gaggawa ta Ukraine, Oleksandr Khorunzhyi, ya shaidawa wani taron manema labarai cewa, hare-hare kusan 190, Rasha ta kai da jirage marasa matuka cikin kwanaki 10 da suka gabata a yankuna 16 na kasar ta Ukraine da kuma birnin Kyiv fadar gwamnatin kasar.

Oleksandr Khorunzhyi ya ce daga faro hare-haren na Rasha zuwa yanzu a kasa da kwanaki 10 sai da ta kashe mutane 70 baya ga jikkata wasu 240 dukkaninsu da taimakon jiragen marasa matuka na Iran.

Tun cikin watan Yulin da ya gabata Amurka ta yi gargadin cewa Iran na shirin taimakawa Rasha da makamai don kai farmaki Ukraine, batun da Iran ke ci gaba da musantawa.

Ko a makon jiya sai da EU ta lafta wasu takunkumai kan Iran bayan zargin kasar da dakile masu zanga-zangar kin jinin hijabi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.