Isa ga babban shafi

An kame mutane fiye da 1200 baya ga kashe wasu 75 a zanga-zangar Iran

Masu zanga-zanga sun yi arangama da jami’an tsaron Iran, yayin da bangarori da dama na kasar da suka hada da malaman jami’a da jarumai da ‘yan wasan kwallon kafa suka nuna goyon bayansu ga zanga-zangar wadda ta barke sakamakon mutuwar Mahsa Amini da ‘yan sandan kula da da'a suka kama ta saboda rashin sanya hijabi.

Wani bangare na masu zanga-zangar kisan Mahsa Amini a Iran.
Wani bangare na masu zanga-zangar kisan Mahsa Amini a Iran. AFP - -
Talla

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Iran IHR ta ce, kawo yanzu sama da mutane 75 ne suka rasa rayukansu tun daga lokacin da zanga-zangar ta barke bayan mutuwar Amini a ranar 16 ga watan nan na Satumba.

Hukumomin Iran sun ce, sun kama fiye da mutane dubu 1 da 200 da suka hada da masu rajin kare hakkin bil’adama da lauyoyi da ‘yan jarida da sauran masu boren.

Ministan Kiwon Lafiya na Iran, Bahram Einollahi ya zargi masu zanga-zangar da lalata motocin daukar marasa lafiya har guda 72, yayin da a gefe guda, ake zargin hukumomin kasar da yin amfani da motocin wajen jigilaar jami’an tsaro a fakaice.

Kungiiyar Kare Hakkin Bil’adaman ta ce, jami’an tsaron kasar sun yi amfani da alburusan gaske da suka harba kai tsaye cikin dandazon masu zanga-zangar, sannan ‘yan sanda kwantar da tarzoma sun yi maka wa masu boren kulake.

A bangare guda, wasu hotunan bidiyo sun nuna yadda ‘yan mata suka yi ta cire tare da keta kallabinsu da sunan nuna bacin rai kan mutuwar Amini da ta mutu a hannun ‘yan sandan kula da da’a bayan sun kamata saboda rashin sanya hijabi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.