Isa ga babban shafi

Adadin mutanen da suka mutu a zanga-zangar kin jinin Hijabi a Iran ya kai 50

Adadin mutanen da suka mutu a zanga-zangar Iran ya karu zuwa mutum 50, cikin mako guda da faro boren bayan kisan matashiya Mahsa Amini da ake zargin jami’an ‘yan sandan tabbatar da bin doka da aikatawa.

Wasu mata yayin zanga-zangar kin jinin Hijabi a Iran.
Wasu mata yayin zanga-zangar kin jinin Hijabi a Iran. AP - Francisco Seco
Talla

Kamfanin dillancin labarai na Borna da ke tabbatar karuwar adadin dai dai lokacin da ake samun karuwar masu shiga zanga-zangar ta kin jinin hijabi a karin birane da dama na kasar.

Kwan ana 8 kenan ana ganin kakkarfar zanga-zangar a manyan biranen Iran ciki har da Tehran don nuna kyamarsu ga takurar da ake musu wajen tilasta su sanya hijabi ba da ra’ayinsu ba.

Tun farko dai zanga-zangar ta samo asali daga kamen Mahsa Amini ‘yar shekaru 22 da jami’an ‘yan sandan tabbatar da bin dokokin addini suka kame amma kuma kwanaki 3 bayan kamen suka sanar da mutuwarta, lamarin da ya sanya zargin ko su suka kashe ta .

Duk da ikirarin da hukumar ‘yan sandan kasar ta yin a cewa matashiyar ta mutu ne sanadiyyar bugun zuciya amma dandazon matasa na ci gaba da zanga-zangar kalubalantar jami’an wadanda ke tilasta sanya Hijabi a sassan kasar.

A wasu yankunan kasar an ga yadda dandazon mata ke wani gangamin kona hijbansu don fusata jami’an.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.