Isa ga babban shafi

Wadanda suka mutu a zanga-zangar Iran sun karu zuwa 31

Alkaluman wadanda suka mutu a zanga-zangar Iran ya karu zuwa mutum 31 bayan arangamar da masu boren ke ci gaba da yi da jami’an tsaro, duk dai kan kisan matashiya Mahsa Amini da ake zargin jami’an ‘yan sandan tabbatar da bin dokokin addini da aikatawa.

Mutane na ci gaba da kone-kone saboda mutuwar Mahsa Amini,
Mutane na ci gaba da kone-kone saboda mutuwar Mahsa Amini, via REUTERS - WANA NEWS AGENCY
Talla

Zuwa yanzu dai zanga-zangar ta fantsama zuwa kusan dukkanin sassan Iran, bayan da tun farko aka faro boren a lardin Kurdistan wato mahaifar matashiyar Mahsa Amini wadda ta mutu lokacin da take tsare a hannun jami’an ‘yan sandan bayan kamata da laifin kin sanya hijabi, lamarin da ya sanya zargin ko jami’an ne suka kashe ta duk da cewa a hukumance sun yi ikirarin cewa matashiya ta mutu ne sakamakon hawan jinni.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Iran ta ce al’ummar kasar sun fito tituna ne don kwatar hakkinsu da ake take musu inda shugaban kungiyar ta IHR ke cewa zuwa yanzu zanga-zangar na gudana a biranen kasar 30 sai dai akwai fargabar yuwuwar jami’an tsaron kasar su fara amfani da salon kame, don kwantar da zanga-zangar.

A cewar kungiyar alkaluman wadanda suka mutu a zanga-zangar ya haura 30 ciki har da mutum 11 da aka kashe a garin Amol a Larabar da ta gabata, da kuma wasu 6 a Babol, yayinda ake ci gaba da arangama tsakanin jami’an tsaro da masu boren.

Tuni dai kasashen Duniya suka fara wadai da kisan Mahsa baya ga tilas din da ake yiwa matan kasar wajen sanya hijabi ba tare da ra’ayinsu ba, yayin da a bangare guda Amurka ta sanar da sanya takunkumi kan jami’an ‘yan sanda bisa tilasta bin dokokin addinin na Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.