Isa ga babban shafi

Masu zanga-zanga sun koma titunan Iran duk da zare idon jami'an tsaro

Al'ummar Iran sun bijirewa gargadin ma’aikatar shari’ar kasar inda suka sake fita kan tituna a daren jiya Lahadi domin nuna rashin amincewarsu kan kisan wata budurwa 'yar Kurdawa Mahsa Amini da suke tuhumar 'yan sanda da yi.

Masu zanga-zanga a Iran.
Masu zanga-zanga a Iran. © REUTERS/Azad Lashkari
Talla

Akalla mutane 41suka mutu tun bayan barkewar tarzomar, akasarinsu masu zanga-zanga, da kuma jami’an tsaron juyin-juya halin kasar ta Iran.

Yayin zanga-zangar da ta zama mafi girma da aka yi cikin kusan shekaru uku a kasar, jami’an tsaro sun yi harbi kai tsaye da harsasai masu kisa kan masu bore, yayin da su kuma suka rika jifan jami’an da duwatsu gami da kona motocin ‘yan sanda da wasu gine-ginen gwamnati.

Rahotanni sun ce mahukuntan Iran sun zafafa kame ‘ya jarida da masu fafutuka a ci gaba da dirar mikiyavda suke wa farar hula da suka fito zanga zangar kin jinin gwamnati.

'Yan jarida 18 ne aka jefa a kurkuku tun da aka fara wannan zanga zanga a farkon watan nan, biyo bayan mutuwar matashiya Mahsa Amini mai shekaru 22 a hannun ‘yaan sandan gyarar hali na kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.