Isa ga babban shafi

Sama da mutum 70 aka kashe a zanga-zangar Iran kawo yanzu

Sama da mutane 75 ne aka kashe a zanga-zangar Iran da ta biyo bayan mutuwar wata matashiya Mahsa Amini a hannun jami’an tsaro, kamar yadda wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta bayyana.

Zanga-zangar na zuwa ne bayan zargin jami'an 'yan sanda da kashe wata matashiya
Zanga-zangar na zuwa ne bayan zargin jami'an 'yan sanda da kashe wata matashiya AP
Talla

Alkaluman da hukumomin kasar suka fitar, sun ce an kashe mutane 41, ciki har da jami’an tsaro da dama.

Sai dai rahoton kungiyar ta kare hakkin bil’adama, ta ce akalla mutane 76 ne aka kashe a rikicin na Iran, adadin da ya karu daga mutane 57 da’a baya aka bayyana mutuwar su.

Zanga-zangar wacce ita ce mafi girma da aka yi a Iran cikin kusan shekaru uku da suka gabata, jami’an tsaro sun yi amfani da tankokin ruwan zafi da kananan alburusai don tarwatsa dandazon mutanen, inda masu zanga-zangar suka yi amfani da duwatsu da kona motocin ‘yan sanda tare da kona gine-ginen gwamnati a matsayin martani, kamar yadda kungiyar ta sanar.

Hukumomi sun ce an kama mutane kusan 450 a arewacin lardin Mazandaran, kari kan mutane 700 da aka bayyana kamawa a ranar Asabar a Gilan, tare da wasu daga wasu yankuna na kasar.

Daga cikin wadanda aka kama akwai 'yan jarida 20, a cewar kungiyar kare hakkin ‘yan jaridu ta duniya CPJ.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.