Isa ga babban shafi

Bangarorin da ke yaki a Yamen sun amince da tsawaita yarjejeniyar zaman lafiya

Bangarorin da ke rikici da juna a Yemen sun amince da tsawaita yarjejeniyar zaman lafiyar da ke tsakaninsu da akalla watanni 2 a nan gaba wanda zai kai har zuwa nan da ranar 2 ga watan Oktoba.

Mayakan 'yan tawayen Huthi na Yemen.
Mayakan 'yan tawayen Huthi na Yemen. AP - Hani Mohammed
Talla

Kafin yanzu dai bangarorin biyu sun kulla yajejeniyar zaman lafiyar ta watanni 4 gabanin sake cimma yarjejeniyar a jiya talata.

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Yemen Hans Grundberg ya bayyana gamsuwa da sabunta yarjejeniyar wadda tuni ta samu goyon bayan kasashen Saudi Arabia da Oman da kuma kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

A jawabinsa Mr Hans ya yabawa jagorancin Yemen da ya taimaka kwarai wajen tabbatar da tsawaita yarjejeniyar da nufin tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Tsawon shekaru 'yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran suka shafe su na yaki da Sojin gwamnatin kasar masu samun goyon bayan hadakar sojin kasashen larabawa bisa jagorancin Saudiyya, yakin da ya haddasa asarar dimbin rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.