Isa ga babban shafi
Taron COP26 A Galasgow

MDD tace yarjejeniyar yanayi da aka cimma da kyar a taron Glasgow na da rauni

Kusan kasashen duniya 200 sun cimma wata yarjejeniyar bai-daya domin yaki da matsalar sauyin yanayi bayan sun kwashe tsawon makwanni biyu suna kiki-kaka kan yarjejeniyar.

Shugaban taron COP26 Alok Sharma da wasu masu halartan taron na Glasgow, Scotland, Britain 13/11/21.
Shugaban taron COP26 Alok Sharma da wasu masu halartan taron na Glasgow, Scotland, Britain 13/11/21. REUTERS - YVES HERMAN
Talla

Duk da cewa, an cimma wannan yarjejeniya da jibin goshi, amma masana kimiya na ganin cewa, har yanzu tana da tawaya domin kuwa ba ta kunshi daukacin abubuwan da ake bukata ba don rage dumamar yanayi baki daya.

Bukatun kasashe matalauta

An soki kasashen duniya mawadata a taron na COP26 da ya gudana a birnin Glasgow saboda nokewarsu wajen samar da kudade ga kasashe matalauta wadanda kuma ke fuskantar barazanar fari da tunbatsar tekuna da tashin gobara da kuma kadawar guguwa a sanadiyar sauyin yanayi.

A yayin cimma yarjejeniyar ta magance sauyin yanayi, kasashen China da India sun hakikance cewa, dole ne a sassauta a bangaren makamashi.

Wakilan kasashen duniya dai, sun shiga tattaunawa da juna a taron ne da zummar dabbaka yarejejeniyar Paris ta 2015 wadda manufarta ita ce, takaita dumamar yanayi da maki 1.5 a ma’aunin Celcius. Sai kuma samar da kudade ga kasashen duniya masu tasowa.

Rashin gamsuwar Majalisar Dinkin Duniya

Tuni Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteress ya yi lale marhabin da yarjejeniyar da kasashen duniyar suka cimma a birnin na Glasgow, amma a cewarsa, har yanzu fa akwai sauran rina-a kaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.