Isa ga babban shafi
COP26-MDD

MDD ta yi watsi da bukatar kungiyoyi kan dage taron yanayi na COP26

Majalisar Dinkin Duniya ta ki amincewa da bukatar wasu kungiyoyin fararen hula n adage taron sauyin yanayin da aka shirya gudanarwa a Birtaniya saboda abinda suka kira rashin samun allurar rigakafin cutar korona ga kasashe masu tasowa kuma hakan na iya yiwa mahalarta taron illa.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson a jawabinsa yayin kaddamar da shirin karbar bakon taron yanayi na COP26 a London.
Firaministan Birtaniya Boris Johnson a jawabinsa yayin kaddamar da shirin karbar bakon taron yanayi na COP26 a London. AP - Chris J Ratcliffe
Talla

Mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya Farhan Haq ne ya bayyana matsayin ta sakamakon bukatar dage taron da aka shirya gudanarwa ranar 31 ga watan Oktoba mai zuwa a Glasgow da ke Scotland, kamar yadda kungiyoyin fararen hula suka  gabatar.

Jami’in yace sun fahimci korafin da kungiyoyin suka gabatar, amma ya zuwa wannan lokaci babu wani canji ko kuma tunannin yin haka.

Akalla kungiyoyin fararen hula 1500 suka gabatar da bukatar dage taron da aka yiwa lakabi da COP26 saboda karuwar masu harbuwa da cutar korona da masu mutuwa da kuma rashin samun maganin rigakafi.

Wannan matsayi na Majalisar yayi daidai da na gwamnatin Birtaniya wadda ke shirin daukar nauyin taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.