Isa ga babban shafi
Sauyin Yanayi

Masifun yanayi sun tsananta a duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, masifu masu alaka da sauyin yanayi sun yi tashin gwauron zabi a cikin rabin karnin da ya gabata, abin da ya haddasa barna mai yawan gaske, duk da cewar duniya ta mallaki fasahohin gargadi na zamani domin rage yawan mace-mace.

Ambaliyar ruwa na cikin jerin masifun da suka addabi duniya a dalilin sauyin yanayi a cewar masana.
Ambaliyar ruwa na cikin jerin masifun da suka addabi duniya a dalilin sauyin yanayi a cewar masana. - AFP/File
Talla

Rahoton da Hukumar Kula da Yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya WMO ta fitar, ya yi nazari ne kan adadin mace-mace da asarar dimbin dukiyar da aka yi sakamakon masifu masu alaka da sauyin yanayi, dumamarsa da kuma saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya a tsakanin shekarun 1970 zuwa 2019.

Rahoton binciken ya kuma gano cewa yawan aukuwar masifun ya ninka har sau biyar a shekarun baya-bayan nan saboda dumamar yanayi.

A jumlace, nau'ukan masifu sama da dubu 11 masu alaka da gurbatar yanayi da dumamarsa suka auku a sassan duniya tun daga 1970 zuwa yanzu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da miliyan biyu da kuma tafka hasarar akalla Dala tiriliyan 3 da biliyan 640.

Binciken kwararrun ya ce, an samu fiye da kashi 91 na mace-macen ne a cikin kasashe masu tasowa, kuma matsalar fari ce sanadin asarar rayuka mafi girma, bayan da ita kadai ta kashe mutane akalla dubu 650, yayin da guguwa ta kashe mutane akalla 577, cikin shekaru 50 da suka gabata.

Ambaliyar ruwa kuwa, ta halaka mutane kusan kusan dubu 59 ne, sai kuma matsanancin yanayin zafi da ya kashe mutane kusan 56,000, a cikin shekarun 50 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.