Isa ga babban shafi
TARON-SAUYIN YANAYI

Masana sauyin yanayi na gudanar da taro a Marseille

Kasashen duniya na shirin gudanar da wani gagarumin taro, da ke da nufin lalubo hanyoyin kare muhalli, da sauyin yanayi da kuma kare hallitu da kuma tsirran da ke rayuwa a doron kasa.

Mahalarta taron sauyin yanayi a Marseille
Mahalarta taron sauyin yanayi a Marseille AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Wannan taron dai na zuwa ne dai-dai lokacin da sauyin yanayi ke ci gaba da haddasa ambaliyar ruwa da sauran masifu a duniya.

Taron da za’a gudanar a birnin Marseille na Faransa zai kasance a karkashin kulawar kungiyar kula da yanayi da hallitu ta duniya kuma zai mayar da hankali wajen tattaunawa kan irin mummunar yanayin da duniya ta tsinci kanta saboda sauyin yanayina da kuma gurbatar muhalli.

Masu rajin kare muhalli na gargadi akan sakacin da ake samu
Masu rajin kare muhalli na gargadi akan sakacin da ake samu DANIEL LEAL-OLIVAS AFP/File

Za a kuma tattauna batun yadda wasu hallitu na duniya ke bacewa a duniya saboda yadda ‘dan Adam ke ganganci wajen gurbata muhalli, da kuma dumamar yanayi da batun barkewar wutar daji.

A cewar masu shirya taron an lura da yadda ake dada tunkarar fadawa cikin mummunan yanayi sakamakon sauyin da ake samu saboda haka dole ne a dauki matakin gaggawa.

Kungiyar ta kula da yanayi ta kuma ce a yayin taron za’a lalubo sabbin hanyoyin sauya dabi’un jama’a na rashin kula da muhalli da kuma yin abubuwan da ka iya janyo sauyin yanayi.

Kungiyar ta kuma kara da cewa duk da taron ya zo a kurarren lokaci amma dai idan an mayar da hankali za’a iya ceto rayukan jama’a ta hanyar managartan shawarwarin da za’a cimma matsaya akansu a karshen sa.

A baya-bayan dai an ga yadda sauyin yanayi ke haddasa manyan bala’o’in da ke hallaka mutane kamar ambaliyar ruwa da narkewar kankara da ke cika tekuna da wutar daji da kwararaowar hamada da kuma mahaukaciyar guguwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.