Isa ga babban shafi
Duniya-Dumamar yanayi

Kungiyoyin dubu 1 da 500 na son MDD ta dage taron yanayi na COP26

Kungiyoyin fararen hula akalla dubu daya da 500 ne suka bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta dage gudanar da taron kasa da kasa kan dumamayar yanayi da ake kira COP26, wanda ya kamata a fara cikin watan nuwamba mai zuwa a birnin Glasgow na kasar Scotland.

Babban taron kan dumamar yanayi na mayar da hankali kan yadda Duniya za ta shawo kan matsalar wadda tuni ta fara yiwa jama'a illa.
Babban taron kan dumamar yanayi na mayar da hankali kan yadda Duniya za ta shawo kan matsalar wadda tuni ta fara yiwa jama'a illa. © Fotomontagem com imagens do ukcop26.org
Talla

A wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar a wannan talata, kungiyoyin sun bayyana cewa lura da halin da duniya ke ciki na fama da annobar covid-19, akwai bukatar dage gudanar da wannan taro da ya kamata ya hada dubban mutane daga sassan duniya.

Kungiyoyin sun bayyana cewa tsadar allurar kariya daga cutar ta Covid-19 da karancin wannan allura, wadannan abubuwa ne da nuni da cewa zai kasance mai wuya taron ya iya samun nasarorin da ake bukata.

Daga cikin kungiyoyin da suka sanya hannu kan wannan kira, har da Climate Action Network, da Greenpeace, WWF, Action Aide, Oxfam da kuma Amnesty International.

Matukar dai aka ce za a gudanar da wannan taro a cikin watan nuwamba mai zuwa kamar dai yadda aka tsara, wakilai daga kasashe da dama ba za sus amu damar halartar shi ba, wannan kuwa lura da cewa Birtaniya ta wallafa jeri kasashe wasu kasashe da al’ummominsu ba su da izini shiga kasar saboda wannan annoba ta korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.