Kasashen Duniya sun gana ta kafar Intanet dangane da canjin yanayi
Wakilan kasashen duniya sun gana ta kafar Intanet domin fara nazari kan wata yarjejeniyar wucen-gadi, gabanin babban taron su kan matsalar sauyin yanayi da aka jinkirta saboda annobar Korona,.
Wallafawa ranar:
Kimanin kasashen duniya 195 suka halarci ganawar ta kafar Intanet wadda ita ce irinta ta farko tun bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da yarjejeniyar wucen-gadin a cikin watan Yuli, yayin da kasashen za su ci gaba da nazartar yarjejeniyar har nan da ranar 3 ga watan Satumba mai zuwa.
Wannan yarjejeniya dai, ta bukaci kare akalla kashi 30 na doran kasa da tekuna da kuma sauran tsirrai da dabbobi.
Yarjejeniyar ta fayyace wa bil’adama tsarin da zai bi wajen tabbatar da zaman lafiya tsakaninsa da sauran halittu nan da shekarar 2050, yayin da ta zayyana wasu kudurori da ake fatan cimma su nan da shekarar ta 2030 domin kare muhallin tsirrai da dabbobi.
Kodayake har yanzu, kungiyoyin masu rajin kare dabbobi da muhalli na duniya na ci gaba da neman alfarma daga hukumomin duniya don ganin sun tsaurara manufofin da yarjejeniyar ta kunsa da suka hada da bukatar bullo da wani tasri da zai hana sake barkewar annobar Coronavirus.
Mataimakiyar shugaban Kungiyar Wildlife Conservation Society, Susan Lieberman ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFPC cewa, ko kadan wannan yarjejeniya ba ta tabo batun Korona ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu