Isa ga babban shafi
Sauyin yanayi

Rahoton sauyin yanayi ya kidima shugabannin duniya

Shugabannin kasashen duniya da kungiyoyin kare muhalli da masu fada-aji, sun mayar da martani game da wani sabon rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi mai cike da tashin hankali.

Kasashen duniya 195 ne suka amince da rahoton mai tayar da hankali
Kasashen duniya 195 ne suka amince da rahoton mai tayar da hankali AMOS GUMULIRA AFP/File
Talla

Rahoton na IPCC  ya yi gargadin cewa, ma’aunin Celsius na yanayin duniya zai kai maki 1.5 nan da shekara ta 2030, lamarin da ke zama babbar barazana ga doran-kasa.

Jim kadan da sakin rahoton, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci cimma matsaya a taron Majalisar Dinkin Duniya na watan Nuwamba  domin tunkarar matsalar ta sauyin yanayi da ta girmama.

Jakadan Amurka kan sauyin yanayi, John Kerry ya ce,  rahoton na nuni da cewa, matsalar na ci gaba da ta’azzara.

Mataimakin shugaban kula da sauyin yanayi na  Kungiyar Tarayyar Tura, Frans Timmermans ya ce, rahoton mai shafuka dubu 3 da 500, ya nuna cewa, an makara a  yunkurin takaita matsalar da kuma dakile ta.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson wadda gwamnatinsa ke shirin karbar bakwancin wani taron sauyin yanyi a cikin watan Nuwamba, ya ce, rahoton na da tayar da hankali kuma ya yi fatan wannan al’amari zai zama tamkar yekuwa ga duniya domin ta daura damara.

Tsohon shugaban Maldives, Mohd Nasheed ya ce, rahoton ya tabbatar da cewa, kasashen da suka fi fama da tasirin dumamar yanayi na gab da shafewa.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce, dole ne a dauki rahoton tamkar kararrawar mutuwa da ke kawo karshen amfani da gawayi da man fetur da iskar gas saboda yadda albarkatun ke ta’annati ga duniyar da muke rayuwa a cikinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.