Isa ga babban shafi
Turai - China

Macron da Markel sun gana da Xi kan sauyin yanayi da hakkin dan adam

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel sun tattauna da takwaransu na China Xi Jin Pin ta kafar bidiyo kan batutuwan da suka shafi sauyin yanayi, kasuwanci da kuma kare hakkin dan Adam.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Angela Merkel shugabar gwamnatin Jamus, tare da shugaban China Xi Jin Pin da kuma shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Turai EU Jean Claude Juncker, a fadar Elysee dake birnin Paris cikin shekarar 2019.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Angela Merkel shugabar gwamnatin Jamus, tare da shugaban China Xi Jin Pin da kuma shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Turai EU Jean Claude Juncker, a fadar Elysee dake birnin Paris cikin shekarar 2019. © EPA-EFE/Thibault Camus / POOL
Talla

Sanawar da fadar gwamnatin Faransa ta fitar ta ce, manufar ganawar shugabannin ta jiya ita ce kokarin cimma matsaya kan banbancin ra’ayin dake tsakanin Turai da China kafin halartar manyan tarukan dake tafe, cikinsu har da taron kasahen duniya kan matsalar dumamar yanayi da Birtaniya za ta karbi bakunci da kuma, taron kasashen kungiyar G20 da zai gudana a birnin Rome na Italiya.

Yadda wata masana'anta ke fitar da gurbatacciyar Iska.
Yadda wata masana'anta ke fitar da gurbatacciyar Iska. JOHANNES EISELE AFP/File

Dangane da matsalar sauyin yanayi, shugaba Macron da Merkel sun gana da Xi Jin Pin na China ne kan muhimmancin kawo karshen tallafin da gwamnatoci ke baiwa cibiyoyi ko masana’antun dake amfani da makamashin kwal dake fitar da gurbatacciyar iska.

Fadar gwamnatin Faransa ta kuma ce shugabannin Turan biyu sun tattauna da takwaransu na China kan batun kare hakkin dan adam da kuma bukatar kao karshen bautar da mutane a kasarsa, abinda kai tsaye ke nufin halin da ‘yan kabilar Uighur ke ciki a yankin Xinjiang dake yammacin kasar ta China.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce ‘yan kabilar Uighur akalla miliyan 1 mafi aksarinsu Musulmi hukumomin China suka killace a sansanonin dake yankin Xinjiang inda suke bautar da su gami da daukar matakan hana su cigaba da haihuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.