Isa ga babban shafi
Faransa - China

China ta bukaci Faransa ta taimaka a gyara huldar kasuwancinta da EU

China ta bukaci Faransa ta sanya baki wajen  rinjayar  Tarayyar Turai ta saka hannu a yarjejeniyar zuba jari da kasuwanci da majalisar dokokinta ta dakile, amma wani ministan Faransar ya ce dole sai Beijin ta fara dage takunkuman da ta kakaba wa ‘yan majalisar Turan.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ta takwaransa na China Xi Jinping yayin wata ganawa a Faransa a watan Maris 2019
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ta takwaransa na China Xi Jinping yayin wata ganawa a Faransa a watan Maris 2019 REUTERS/Jean-Paul Pelissier
Talla

Kungiyar Tarayyar Turai da China sun amince da wata yarjejeniyar kasuwanci a karshen shekarar da ta gabata, bayan shekarau 7 na zazzafar tattaunawa da taimakon Jamus.

Amma a makon da ya gabata, majalisar dokokin Tarayyar Turai ta kada kuri’ar kin amincewa da yarjejeniyar idan har takunkuman da China ta kakaba wa ‘yan majalisar suka ci gaba da wanzuwa.

China ta caccaki Turai, kana ta kare matsayintaa na sanya takunkuman, inda ta ce martani ne da ya dace da hukuncin da Turan ta wa jami’anta, a kan zargin take hakkin dan adam da ke gudana a yaankin Musulman Xinjiang, zargin da China ta musanta, tana mai cewa sana’o’i take koya musu a sansanin da ta kai su.

Ministan kasuwanci na China Wanga Wentao, ta wani taron bidiyo da suka yi da takwaransa na Faransa Franck Riester a farkon wannan  makon, sun tattauna wannan batu, inda suka bayyana fatan bijirowa da masalaha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.