Isa ga babban shafi
Sauyin yanayi

Lokaci ya kure wa duniya na magance dumamar yanayi

Wani sabon rahoto da aka wallafa a yau Litinin, ya bayyana takaicinsa kan yadda kasashen duniya suka yi watsi da gargadin da kwararru suka yi musu kan tasirin sauyin yanayi wanda ke haddasa mabanbantan musibun da ake gani a yanzu. Rahoton ya bayyana cewa, lokaci ya kure wa kasashen duniya dangane da magance wannan matsalar ts sauyin yanayi cikin kankanin lokaci.

Matsalar sauyin yanayi ta jefa kasashen duniya cikin bala'i
Matsalar sauyin yanayi ta jefa kasashen duniya cikin bala'i Dimitar DILKOFF AFP
Talla

Rahoton ya bayyana cewa, yanzu haka matsalar dumamar yanayi ta fara yin ramuwar gayya ga wannan doran-kasan da muke kai, wanda zai sa ma’aunin yanayi na Celsius ya kai maki 1.5 nan da shekarar 2030.

Rahoton wanda Majalisar Dinkin Duniya ta yi nazari  a kansa, na zuwa ne kwanaki 90 gabanin wani taron kasashen duniya kan matsalar ta sauyin yanayi a birnin Galsgow.

Rahoton ya kara da cewa, dumamar yanayin za ta yi kamari nan da shekara ta 2050 koda kuwa al’ummar duniya sun ci gaba da mutunta tsarin takaita gurbata muhalli.

Kasashen duniya 195 ne suka amince da wannan rahoton wanda ya haskaka wa gwamnatoci matakan da ya dace su dauka duk da cewa, suna jinkirin tunkarar matsalar.

A halin yanzu dai, dumamar yanayin duniya kan ma’aunin Celsius na da maki 1.1 ne, kuma ana ganin wannan lamari na da nasaba da musibun da suka afka wa wasu kasashen duniya a baya-bayan nan, kamar Canada wadda ta yi fama da mugun zafi da kuma China da Jamus da suka gamu da gagarumin ibtila’in ambaliyar ruwa, sai kuma  wuatar daji  da ta addabi Girka da California.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.