Isa ga babban shafi
Muhalli - Canjin Yanayi

'Mai yiwuwa matsalar dumamar yanayi ta yi munin da ba za a iya mangance ta ba'

Jagoran wata tawagar kwararru ta kasa da kasa a fannin Kimiyya da Muhalli, Markus Rex yayi gargadin cewar mai yiwuwa matsalar dumamar yanayi da ta saka duniya a gaba, ta kai matsayi ko munin da ba za a iya shawo kanta ba.

Yadda tsaunin kankarar Esmarkbreen dake kan tsibirin Spitsbergen dake arewacin kasar Norway. 24 ga Satumban 2020.
Yadda tsaunin kankarar Esmarkbreen dake kan tsibirin Spitsbergen dake arewacin kasar Norway. 24 ga Satumban 2020. © REUTERS/Natalie Thomas/File Photo
Talla

Markus Rex ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da kashin farko na rahoton da ya jagoranci  tattarawa tare da wasu kwararru 300 daga kasashe 20, wadanda suka zagaya yankunan Arctic wato karshen duniya daga bangaren arewaci.

Curin kankarar dake narkewa akan tekun Arctic. 14/9/2020.
Curin kankarar dake narkewa akan tekun Arctic. 14/9/2020. via REUTERS - Natalie Thomas

Tawagar kwararrun kan kimiyya da ta zama mafi girma da aka tura rangadi zuwa yankunan karshen duniya daga arewaci ta ce tsunukan kankara da kuma kankarar da ta malale tekuna na narkewa cikin yanayin sauri mai ban tsoro fiyde da kowane lokaci a tarihin duniya.

Tawagar masanan da aka kashewa dala miliyan 165 wajen daukar nauyinta ta shafe kwanaki 389 tana ratsa yankunan Arctic da dama kafin komawa Jamus a watan Oktoban shekarar da ta gabata, tare da rahoto mai yawan gaske da ya lakume sararin adana bayanan da girmansa gami da nauyi ya kai terabyte 150, sai kuma na’u’ikan kankara siye da dubu 1.

Karamin tsaunin kankara akan tekun Arctic.
Karamin tsaunin kankara akan tekun Arctic. © REUTERS/Natalie Thomas/File Photo

Muhimman abubuawan da kwararrun suka maida hankali wajen tattara bayanai akai sun hada da alakar zamantakewa tsakanin Halittu da Muhalli, tekuna, da kuma kankara dake daskarewa akansu da kuma yanayin iskar dake zagaye da duniyar mu da a turance ake kira da Atmosphere.

Ga al’ada dai yankin Arctic mai tsananin sanyi kan kasance da kankara a malale hatta akan tekuna ko da kuwa bayan an shiga yanayi na zafi, amma a wannan karon masanan masanan sun ce ba ahaka abin yake ba, dan haka suka yi gargadin nan da wasu ‘yan shekaru za a iya neman kankarar ma a rasa musamman a tekuna, abinda ke nufin za su tumbatsa daga nan kuma sai masifun ambaliya hade da guguwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.