Isa ga babban shafi
Sauyin yanayi

Shugabannin duniya sun bukaci kara kaimi wajen shawo kan sauyin yanayi

Shugabannin Kasashen duniya sun bukaci kara kaimi wajen daukar matakan kare muhalli da kuma gabatar da bukatar sanya kowacce kasa ta duniya cikin shirin samar da muhalli mai inganci a taron da ya gudana a Koriya ta Kudu.

Hayakin dake haifar da gurbata muhalli
Hayakin dake haifar da gurbata muhalli Ina FASSBENDER AFP/File
Talla

Sauyin yanayi na daga cikin manyan kalubalen dake yiwa cigaban duniya barazana wanda ya kunshi karancin samun amfanin gona da yanayi mara kyau dake yiwa tattalin arzikin kasashen dake karbar yan yawon bude ido ila da haifar da yaduwar cututtuka da kuma wasu matsaloli na daban.

Koriya ta kudu da ta bayyana aniyar shirin rage kudaden da take kashewa wajen amfani da gawayi, na bukatar ganin an samu cigaba ta wannan bangaren a fadin duniya.

Shugaba Moon Jae-In ya shaidawa taron da aka gudanar ta bidiyo cewar zata taka rawa wajen hada kan kasashen da suka cigaba da masu tasowa a taron dake mayar da hankali kan hadin kai tsakanin gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kan su.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci kasashen duniya da su kawo karshen amfani da man fetur, inda take cewa yana haifar da gurbata muhallin dake barazana ga rayukan jama’a da kuma tattalin arzikin su kamar annobar korona.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson yace lokaci yayi da kowacce kasa at duniya zata cika alkawarin da ta dauka na kare muhalli.

Shugabannin sun jaddada muhimmancin tafiya da kasashe matalauta, yayin da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci kasashen Afirka da su zuba jari wajen samun makamashi na zamani maimakon cigaba da dogaro da man fetur domin tafiya da sauran kasashen duniya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guteres yace shawo kan matsalar gurbata muhalli zai taimaka wajen kare lafiyar jama’a, amma ya zama dole a tafi da kowanne bangare ba tare da nuna banbanci ba.

Bankin Duniya yayi hasashen cewar akalla mutane tsakanin miliyan 32 zuwa 132 zasu fada cikin tsananin talauci nan da shekarar 2030 sakamakon illar sauyin yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.