Isa ga babban shafi
Sauyin Yanayi

Masana kimiya na son a dauki matakin gaggawa kan sauyin yanayi

Masana kimiyya fiye da 200 sun bukaci taron kasa da kasa kan sauyin yanayi na COP26 da ya dauki matakin gaggawa don dakatar da dumamar yanayi. Cikin wata budaddiyar wasika da suka aike, masanan sun yi gargadin cewa, za a shafe daruruwan shekaru ba tare da janyewar wasu daga cikin tasirin sauyin yanayi ba.

Wani bangare na mahalarta taron sauyin yanayi a birnin Glasgow.
Wani bangare na mahalarta taron sauyin yanayi a birnin Glasgow. AP - Alberto Pezzali
Talla

Babbar manufar taron sauyin yanayin na Glasgow dai ita ce tabbatar da fara aiwatar da yarjejeniyar yaki da dumamar yanayin da aka cimma a birnin Paris, ta yadda za a iyakance yanayin zafin duniya a tsakanin maki digiri 1.5 zuwa 2 a ma’aunin Celcius.

Sai dai yayin da tattaunawar kasashe a taron na COP26 ta shiga kwanaki na karshe, alkawurran da aka yi ya zuwa yanzu na iya haifar da mummunan bala'in karuwar dumamar yanayin zuwa maki 2.7 a ma’aunin Celcius nan da shekara ta 2100, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

A cikin watan Agusta, wani rahoto mai tsoratarwa daga Hukumar Kimiyar Yanayi ta Duniya IPPC, ya yi gargadin cewa matsakaicin zafin duniya zai iya kaiwa matakin maki 1.5 a ma’unin Celcius a shekarar 2030, shekaru goma kafin lokacin da kwararru suka yi hasashen zuwansa.

Hukumar ta IPPC ta kara da cewar, domin dakile kazancewar matsalar dumamar yanayi, dole hukumomi su rage hayaki ko iska mai gubar da suke bulbularwa  da akalla kashi 45 cikin 100 nan da shekaru goma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.