Isa ga babban shafi
Yanayi-Duniya

Lokaci ya kurewa Duniya a kokarin samun kariya daga bala'o'in sauyin yanayi

Majalisar Dinkin Duniya ta yi ikirarin cewa alkawarin India yayin taron yanayi na COP26 a Glasgow babban abun maraba ne a kokarin da ake na yaki da dummar yanayi dai dai lokacin da illolinta suka fara yiwa Duniya barazana.

Rahoton masana ya nuna cewa ko da an dauki mataki a yanzu akwai yiwuwar duniya ta fuskanci tsananin zafin da aka yi hasashe a shekaru kalilan masu zuwa.
Rahoton masana ya nuna cewa ko da an dauki mataki a yanzu akwai yiwuwar duniya ta fuskanci tsananin zafin da aka yi hasashe a shekaru kalilan masu zuwa. AIZAR RALDES AFP
Talla

Alkaluman da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya yi maraba a matakin India na daina fitar da sinadarin na Carbon nan da shekarar 2070, wanda ta ce zai taimaka wajen rage karuwar zafin da Duniya ke gani.

Shirin muhalli na Majalisar Dinkin Duniya UNEP ya ce matakin kasashen na kayyadaddun gudunmawarsu ta fuskar kimiyya fasaha da kuma tattalin arziki ya kara yawan zafin da Duniya ke gani da maki 2.7 wanda ke matsayin babbar barazana ga halittun ban kasa.

Acewar UNEP akwai bukatar rage zafin da Duniya ke gani zuwa maki 1.5 don cimma matsayar da aka kulla karkashin yarjejeniyar yanayi ta Paris.

Shirin na UNEP ya koka da cewa ko da kasashen sun cika alkwurran da suka dauka yayin taron Glasgow akwai yiwuwar matakin da aka kai wajen gurbata muhalli ya yi tasiri ga duniya idan har nan da shekarar 2030 ba a samar da gagaruman sauyi kuma cikin gaggawa don tunkarar matsalar ba.

Shirin ya bukace zaftare yawan sinadaran Carbon din da kasashe ke fitarwa da akalla rubanye 7 matukar ana bukatar ceto duniya daga halin da ta samu kanta a ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.