Isa ga babban shafi
Duniya - Sauyin yanayi

Tudun teku na iya karuwa da kafa 40 saboda sauyin yanayi - Kwararru

Kwararru sun yi gargadin cewa shiga taron sauyin yanayi na Duniya a Glasgow, cike da burin a yi ko mutu, don takaita dumamar yanayi zuwa maki 1.5 a ma'aunin  Celsius, ba shi ne abin damuwa ba.

Wani yanki na tsaunukan kankarar dake yammacin karshen duniya a yankin Antarctica.
Wani yanki na tsaunukan kankarar dake yammacin karshen duniya a yankin Antarctica. AFP/File
Talla

A cewar su, masifun da duniya ke gani a yanzu na ambaliya, da wutar daji, da tsanantar zafi, kamar Saniya ce da kahonta aka gani amma gangar jikin na baya.

Daraktan Cibiyar Kula da Tsarin wanzuwar lamurran yanayi da muhalli na Duniya a Jami'ar Exeter dake Ingila Tim Lenton,  ya ce babban abinda ke hana masana kimiyya barci a halin yanzu shi ne fargabar yadda ayyukan dan adam ka iya haddasa dumamar yanayi kaiwa makura abinda zai janyo barkewar bala’o’I babu kakkautawa.

Wadannan bala’o’in kuwa sun hada da narkewar dubban tsaunukan kankarar dake yankunan Greenland da yammacin Antarctica, abinda ko shakkah babu zai haddasa tumbatsar tekuna ta yadda tudunsu zai karu da fiye da mitoci goma sha biyu kwatankwacin kafa 40 kenan.

Masanan sun kara da gargadin cewa muddin dan adam bai daina bulbalar da sinadarai masu cutar da yanayi ba, to fa dumamar iska ko yanayin zai kone Amazon wanda shi ne daji mai surkukin itatuwa mafi girma a duniya, wanda kuma dan adam ya dogara da shi don shanye gurbatacciyar iskar carbon, kana ya samar masa iskar Oxygene, kamar yadda aka tabbatar a kimiyyance.

Wata boyayyar barazana kuma da duniyar mu a yau ke fuskanta sakamakon dumamar yanayi ita ce karewar wani nau’in kasa mara zurfi mai suna Permafrost, da galibi ake samunta a yankin Siberia dake Rasha. Kasar ta Permafrost dai na rike ne da ninki biyu na adadin iskar gas mai guba da tuni ta kwarara cikin Atmosphere, wato jakar Iskar dake zagaye da duniyar da muke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.